Labarai
Kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya wani fili mallakar tsohuwar ministar man fetur
Wata babbar kotun tarayya da ke Lagos ta ba da umarnin mallakawa gwamnatin tarayya wani fili da ke unguwar Lekki a jihar Lagos, mallakin tsohuwar ministar man fetur Diezani Allison Madueke na wucin gadi.
Filin mai lamba goma sha uku da ke rukunin gidajen Oniru Chieftaincy Private Family Estate a unguwar Lekki, an masa kudi akan naira miliyan dari uku da ashirin da biyar da dubu dari hudu.
Da yake ba da hukuncin alkalin kotun mai shari’a Babs Kuewumi, ya ce, hujjojin da hukumar EFCC ta gabatar gaban kotun ya gamsar da shi a don haka ya sanya shi daukar matakin mallakawa gwamnatin tarayya filin na wucin gadi.
Tun farko da ya ke mika bukatar mallakawa gwamnatin tarayya filin, lauyan hukumar EFCC Mr Anslem Ozioko, ya ce, suna da kwararan hujjoji da suka nuna cewa tsohuwar ministar ta sayi filin ne da kudaden haramun.
Alkalin kotun ya kuma bukaci duk wani da ke ikirarin cewa filin mallakin sa ne, da ya kawo hujjojin hakan cikin sati biyu.