Labarai
Kotu ta raba aure saboda zargin yin garkuwa da mutane
Kotun shari’ar musulunci a nan Kano karkashin mai sharia Munzali Tanko ta raba auren wata mata da mijinta saboda zarginsa da laifin garkuwa da mutane.
Tun da fari dai an tsare magidancin sama da shekara 4 a gidan gyaran hali sakamakon laifin.
Mahaifin matar Malam Ja’afar ne ya buƙaci ƴar ta sa Asma’u da ta shigar da ƙara kan buƙatar mijinta Abdulmumin ya saketa saboda zarginsa da akeyi da laifin garkuwa da mutane.
Sai dai a zaman kotun na ranar Talata mai shari’a ya tambayi Asma’u kan abinda mahaifinta suke buƙata na sakin ta amma ta ce “Ina son mijina kuma ba na buƙatar mu rabu koma a cikin wane irin hali yake a yanzu zan iya zama da shi”.
A nan ne mai shari’a ya waiwayi wanda ake ƙara wato Abdulmumini kan lamarin inda ya ce “Ina kan abinda mata ta ke so, kuma a shirye nake na yi mata duk abinda ta ke so”.
Sai dai daga bisani mai shari’a ya sake waiwayar matar kan buƙatar iyayen na ta na neman saki a wajen mijin na ta.
Kuma Asma’u ta amince mijin ta ya saketa cikin yanayin kuka, kuma nan ta ke mijin yayi mata saki biyu.
You must be logged in to post a comment Login