Labarai
Kotu ta sake cin tarar hukumar KAROTA
Babbar kotun jiha mai lamba 15 karkashin mai shari’a Nasiru Saminu ta yi watsi da bukatar hukumar KAROTA na ta dakatar da aiwatar da hukuncin hana goyon babur mai kafa biyu.
A zaman kotun na yau, mai shari’a Nasiru Saminu ya ki amincewa da bukatar ta su, inda kuma ya yankewa hukumar ta KAROTA tarar naira dubu goma bisa bata mata lokaci.
Tun da fari dai kotun ta bukaci hukumar KAROTA da ta biya tarar naira miliyan daya da dubu dari shida ga wasu mutum biyu da suka yi zargin cewa jami’an hukumar sun kama su a kan laifin yin goyo.
Guda daga cikin masu shigar da kara Kwamared Bello Basi ya tabbatarwa da Freedom Radio cewa, kotun ta saurari bukatar hukumar KAROTA, sai dai bayan nazari ta yi watsi da bukatarsu, ta kuma ci tarar su naira dubu goma.
You must be logged in to post a comment Login