Labarai
Kotu ta sake tabbatar da Ɗanzago a matsayin shugaban jam’iyyar APC a Kano
Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta tabbatar da rushe zaɓen shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kano da ɓangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gudanar.
Alkalin kotun Justis Hamza Mu’azu ya kuma tabbatar da zaɓen shugabancin jam’iyyar ɓangaren tsohon gwamna Sanata Ibrahim Shekarau a ranar Juma’a.
Idan za’a iya tunawa a ranar 30 ga watan Nuwamba, kotu tayi hukuncin cewa zaɓen da ɓangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gudanar haramtacce ne.
Tunda fari dai, ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau sun nemi kotun ta ayyana zaɓen da ɓangaren gwamna Ganduje da suka gudanar a matsayin haramtacce, inda ɓangaren gwamna Ganduje suka hanzarta garzaya kotu domin ɗaukaka ƙara.
Sai dai a hukuncin na ranar Juma’a, kotun ta kori karar ta su, ta kuma nemi su biya abokan sharia’ar ta su naira miliyan ɗaya saboda ɓata musu lokaci da suka yi.
You must be logged in to post a comment Login