Labarai
Kotu ta umarci Ganduje daya mayar da Barista Muhyi kan mukaminsa
A jiya ne kotun da’ar ma’aikata ta Najeriya da ke zamanta a Kano ta baiwa gwamnatin Kano umarnin mayar da tsohon shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa Barista Muhuyi Magaji Rimingado kan mukaminsa har zuwa kammala sauraron karar da ke gabanta.
Hakan na cikin hukuncin da mai shari’a Edward Esele ya zartar, inda ya ce a yanzu Muhuyi zai ci gaba da rike mukaminsa bayan sauke shi da gwamnatin Kano ta yi a kwanakin baya.
Da yake karin haske kan yadda zaman ya kasance Barista Yusuf Ali Faragai wanda shi ne lauyan Barista Muhuyi Magaji ya yi bayani kamar haka.
Barista Yusuf Ali Faragai kenan da yayi karin bayani kan yadda hukuncin kotun da’ar ma’aikata ta yi na mayar da Muhuyi Magaji Rimingado kan mukaminsa na shugabancin hukumar Anti-Kwarafshin bayan sauke shi da gwamnatin ta yi.
Haka kuma kotun ta sanya ranar 7 ga watan Maris domin ci gaba da sauraren shari’ar.
Rahoton:Halima Wada Sinkin
You must be logged in to post a comment Login