Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta yanke wa ƴan Vigilante 5 hukuncin kisa a Kano

Published

on

Babbar Kotun jihar Kano mai Lamba daya karkashin jagorancin Mai sharia Dije Abdu Aboki, ta yanke wa wasu mambobin kungiyar Sintiri ta Vigilante hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun ta yanke musu hukuncin ne bayan da ta same su da laifin kashe wani matashi a unguwar Samegu da ke yankin sabon Titin Panshekara.

Kotun ta zartar musu da hukuncin ne da yammacin Alhamis ɗin makonan.

A baya dai an gurfanar da mutanen bisa kunshin tuhumar hadin baki domin aikata laifi da kuma kisan kai inda suka hallaka matashin Ahmad Musa da akafi Sani da Halifa.

Mutanen su ne: Emanuel Korau da Elisha Ayuba da Iremiya Timothy da Auwal Ja’afar da kuma Mustapha Haladu,.

Da ta ke yanke hukunci Mai shari’ar ta yi karatun baya da ta same su da Laifin kana ta yankemusu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!