Labarai
Kotu ta yanke wa Dagaci da abokinsa hukuncin rataya

Wata Babbar Kotu a jihar Gombe, ta yanke wa Dagacin Gundumar Bangunji, Sulei Yerima, da Shedrack Aliyu hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun su da laifin aikata kisan kai.
Kotun mai lamba 8 da ke zamanta a Gombe, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Abdulsalam Mohammad, ta ce an same su da laifi ne bayan an tabbatar da tuhumar da ake yi musu.
A hukuncin da ya yanke, alƙalin kotun ya kuma wanke tare da sallamar wasu mutum uku sakamakon rashin isassun hujjoji a kansu
Tun da farko, an gurfanar da mutanen a gaban kotu ne, bisa laifukan haɗa baki, tayar da hankali, jikkata mutum, da kisan kai.
A ƙarshe, kotun ta yanke wa Dagacin Bangunji, Sulei Yerima, da Shedrack Aliyu Kwan hukuncin kisa ta hanyar rataya.
You must be logged in to post a comment Login