Ƙetare
Kotu ta yanke wa Sheikh Hasina hukuncin kisa bisa bada umarnin murkushe zanga-zangar dalibai

Kotun International Crimes Tribunal, wadda ke gudanar da shari’un laifukan yaƙi a Bangladesh, ta yanke wa tsohuwar Firayim Minista, Sheikh Hasina, hukuncin kisa bisa zargin bada umarnin murkushe zanga-zangar dalibai ta 2024 da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Alkalin kotun, Golam Mortuza Mozumder, ya ce ana tuhumar ta da laifuka uku, ciki har da tayar da fitina, bayar da umarnin kisa, da kuma kasa dakatar da aikata ta’addancin da aka tafka.
A cewar alkalin am yanke mata hukunci guda ɗaya wanda shi ne hukuncin kisa
Inda kuma Sanarwar hukuncin ta haifar da farin ciki hadi da tafi daga jama’ar da ke cikin harabar kotun.
You must be logged in to post a comment Login