Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kotu ta yankewa Karin Benzema hukuncin zaman gidan Yari na shekara Ɗaya

Published

on

Dan wasan gaba na kasar Faransa da kungiyar Real Madrid dake kasar Spaniya Karin Benzema zai kwashe shekara 1 a gidan Yari, tare da biyan tarar dala 84.

Hakan na zuwa ne bayan da kotu ta tabbatar da samun sa da laifin yada wani faifan bidiyo na abokin wasansa Mathieu Valbuena a shekarar 2015.

Kotun dai ta yanke hukuncin ne a zaman data gudanar a yau Laraba 24 ga watan Nuwambar 2021.

A cewar ta laifin ya saba da dokar hukumar kwallon kafa ta kasar.

Dan wasan mai shekaru 33 ya yi amfani da wannan dama yana neman takawaran nasa na faransa akan ya biya shi wasu kudade,

Sai dai Benzema ya musanta wannan zargi da ake masa, inda yace yana kokarin taimakon dan wasan ne kan takaddamar dake cikin faifan bidiyon.

Sai dai alkalinsa ya ce za su daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yi.

A baya bayan nan Benzema ya dawo wakiltar faransa a wasanninta na kasashe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!