Labarai
Kotu ta yankewa matasa hukuncin shekara 16 bisa laifin damfara
Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 4 da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako karkashin jagorancin mai shari’a Yusuf Muhammad Ubale, ta zartar da hukuncin dauri ga wasu mutane biyu da ta kama da laifin fashi da makami.
Mutanen da suka hada da Lawrence Nwora da kuma Sunday David, an kama su da bindiga a hannunsu kirar Pistol, inda suka yi wa wani mai suna Alhaji Tukur Umar fashin kudi naira miliyan 2 da dubu 39, bayan ya fito daga wani Banki a unguwar Bompai a nan Kano.
Mutanen sun aikata laifin ne a ranar 28 ga watan Janairun shekarar 2011, laifin da ya saba da sashe na 97 da na 298 na kundin hukunta laifuka na Penal Code.
Mai gabatar da kara Barista Dalhatu Dada ya gabatar da shaidu guda biyar, yayin da wadanda ake karar suka kare kansu da kansu.
Mai shari’a Yusuf Muhammad ubale ya yankewa mutanen biyu hukuncin daurin shekaru goma sha biyar-biyar tare da tarar naira dubu 130 kan laifin fashi da makami.
Sai kuma hukuncin daurin watanni shida-shida ko kuma biyan tarar naira dubu 20 kan laifin hadin baki domin aikata laifi.
You must be logged in to post a comment Login