Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta yankewa matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

Published

on

Babbar kotun jihar Kano da ke zaman ta a Miller Road ta yankewa wani matashi Nura Muhammad da aka fi sa ni da Gwanda hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Wannan ya biyo bayan samun Nura da kisan wani matashi mai suna Mudan Muhammad a unguwar Fagge.

Da take yanke hukuncin a Alhamis din nan, mai shari’a Aisha Muhammad ta ce, an samu Nura da laifin kisan kai karkashin sashi na dari biyu da sha biyu (A).

Tun da fari lauyan gwamnati Barista Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ne ya shigar da kara gabam kotun, kuma sun gabatar da shaidun su gida uku.

Sai dai mai shari’a ta yi sassauci bayan da lauyan wanda ake kara Najib Hamisu ya nema, inda hukuncin ya koma kisan kai ta hanyar rataya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!