Kiwon Lafiya
Kotu ta yankewa shugaban kungiyar direbobin hanya ta kasa reshen jihar Lagos hukuncin kisa
Wata babbar kotun tarayya dake zama a Ikeja dake jihar Lagos, ta yanke hukuncin kisa ga Saheed Arogundade, shugaban kungiyar direbobin hanya ta kasa reshen jihar Lagos, saboda kashe wani dan sanda Gbenga Oladipupo mai shekaru 32.
Kamfanin dilancin labaru na kasa NAN ya rawaito cewa mai shari’a Olabisi Akinlade ta kama Arogundade da laifin kisa tare da wasu mutum 5 da suka hada Mustapha Layeni da Adebayo Abdullahi da Seyi Pabiekun da Sikiru Rufai da Yusuf Arogundade.
A yayin yanke hukuncen da ya kwashe awa 3 ana yi da aka kafara da misalin karfe 2 da rabi, mai shair’a Olabisi ta ce wanda ake zargi ya gaza bada hojojin da kotu zata gamasu bas hi ya aikata kisan ba.
Haka zalika Kafin yanke hukuncin, mai shari’ar saboda dalilan tsaro ta nemi a kule akwatin da ake zargin mai laifi na tsaya wa a ciki, a kuma ajiye mukin cikin wani akwati bayan kammala hakan ne, ta bayyana cewar kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin d aya aikata.