Connect with us

Kiwon Lafiya

Kotun da’ar ma’aikata ta dage lallai dakataccen babban jojin kasa ya bayyana gaban kotu

Published

on

Kotun da’ar ma’aikata ta dage kan cewar sai lalle dakataccen babban jojin kasar nan Walter Onnoghen ya bayyana a gaban kotun akan zargin da ake masa na rashin bayyana kadarorin da ya malaka.

Akalin kotun Danladi Umar ne ya bada umarnin a yayin cigaba da zaman shari’ar jimkadan bayan da bangarorin 2 suka amince da a dage cigaba da shari’ar zuwa 13 ga watan nan da muke ciki na Fabareru.

Mai shari’a Danladi Umar ya ce karkashin dokar hukunta masu cin hanci da rashawa, duk wanda lauya yake karewa, sai ya bayyana a kotu kafin wanda ake karar zai bada uzuri na rashin zuwan sa kotu.

 A dai jiya ne a yayin cigaba da sauraran karar, jami’an kotun da’ar ma’aikatar suka sanar da cewar dakataccen babban jojin Najeriya bai halacci zaman ba, a don haka ne alkalin kotun ya dage kan cewar sai ya zo da kan sa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!