Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar gwamna Inuwa Yahaya

Published

on

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja a yau Alhamis ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya.

Idan za a iya tunawa dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta bayyana Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar bayan ya samu kuri’u 342,821 inda ya doke abokin takararsa Jibrin Barde na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 233,131.

A bisa rashin jin dadinta da sakamakon zaɓen, jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa ba a sake zaben Yahaya da mafi rinjayen kuri’u ba.

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa, APC ta gudanar da aringizon kuri’u a rumfunan zabe daban-daban a kananan hukumomi 9 daga cikin 11 na Jihar.

Amma kotun sauraron kararrakin zabe ta yi watsi da karar ta jam’iyyar PDP.

Rashin gamsuwa da hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben yasa, dan takarar PDP da jam’iyyarsa suka garzaya kotun daukaka kara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!