Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano ya bukaci yan siyasa su rika tausasa kalama su

Published

on

Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya buƙaci ‘yan siyasa da su rika tausasa kalamansu yayin yakin neman zaben da ke karatowa.

Sarkin ya bukaci haka ne a yau Litinin, yayin da ya karbi bakuncin dan takarar gwamnan kano na jam’iyar NNPP Abba Kabir Yusuf a fadarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma jaddada cewa duk wanda Allah ya nufa da zama gwamna ya yi kokari wajen cika wa al’umma alkawarin da ya dauka.

Haka kuma ya gode wa dan takarar bisa ziyarar da ya kai masarautar da kuma dukkanin masarautun Kano.

A nasa jawabin, dan takarar gwamnan na jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf ya ce, mutukar ya kasance a matsayin gwamnan Kano zai fi mayar da hankali ne wajen habbaka harkar kasuwanci, ilimi da lafiya da sauran muhimman bangarori.

Shi ma dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADC Sheikh Ibrahim Khalil, ya ziyarci fadar Sarkin na Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!