Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun kolin Nijeriya ta tabbatar da Saddiq Wali a matsayin dan takarar gwamna a PDP

Published

on

A jiya ne kotun kolin kasar nan ta kori ƙarar da Mohammed Abacha ya ɗaukaka gabanta, inda ta tabbatar da Saddiq Wali a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar PDP.

Idan za a iya tunawa a watan jiya ne, kotun daukaka kara a Kano ta jingine wani hukuncin Babbar Kotu, inda ta ce ba Mohammed Abacha ne ɗan takarar PDP ba, abin da ya sanya shi ɗaukaka shari’a zuwa Kotun Ƙoli.

A zantawar Freedom Radio da Sadiq Aminu Wali ya shaida cewa hukuncin ya zo a daidai lokacin da suke bukatarsa.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/03/LABARAN-RANA-WALI-KOTU-HAU-A-02-03-2023.mp3?_=1

Shi ma lauyan Sadiq Wali din Barista Baba Lawan ya shaida yadda zaman kotun ya kasance.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/03/LABARAN-RANA-WALI-KOTU-HAU-B-02-03-2023.mp3?_=2

Wanna na zuwa ne kwanaki 9 gabannin zaben gwamnoni da za a gudanar a fadin kasar nan, wanda kuma dukkanin bangarorin biyu suke neman kujerar gwamnatin Kano karkashin jam’iyyar PDP.

Rahoton: Madeena Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!