Labaran Kano
Kotun sauraron kararrakin zaben ‘yan majalisun jihar Kano dana tarayya sun kammala zama
Kotun sauraron kararrakin zaben majalisun dokokin Jiha da na tarayya da ke zamanta nan Kano ta kammala zamanta baki-daya bayan sauraron kararakkin zabe guda talatin da biyar.
Yayin zaman Kotun na karshe jiya, mai shari’a Ajoke Adepoju ta zartas da hukunci kan karar da ‘dan takarar majalisar jiha na jam’iyyar PDP a karamar hukumar Wudil Ado Mohammed Wudil ya shigar, yana kalubalantar nasarar da Nuhu Abdullahi Achika na jamiyyar APC ya samu a zaben da aka gudanar ranar 9 ga watan Maris din da ya gabata.
Mai Shari’a Ajoke ta ce masu karar sun gaza gamsar da kotu da kwararan hujjojin kariya, a don haka ne ta ayyana Nuhu Abdullahi Achika na APC a matsayin wanda ya samu nasara da kuri’u mafiya rinjaye.
A karamar hukumar Fagge kuwa dan takarar jam’iyyar APC Yusuf Abdullahi Ata ne ya shigar da kara yana kalubalantar nasarar da ‘dan takarar jamiyyar PDP Tukur Muhammad ya samu, inda ya yi zargin cewa takardun makarantar da ya gabatarwa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na bogi ne.
Da ta ke karanto hukuncin mai shari’a Ajoke Adepoju ta ce Yusuf Ata da kuma APC sun gaza gamsar da kotu da hujjojin da za su nuna cewa takardun makarantar Tukur Muhammad na bogi ne, a don haka ne ta tabbatarwa Tukur din nasarar da ya samu.