Labarai
Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta ware ranar da zata saurari karar Jami’yyar PDP
Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta ware ranar da zata saurari korafin da jam’iyyar PDP ta shigar gaban ta, na bukatar ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta bayar da dama a shiga kundin ajiye bayanan ta na sakamakon zaben shugaban kasa.
Jam’iyyar PDPn dai ta roki kotun da ta umarci INEC ta bayar da damar bude runbun ajiye bayanan sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar ashirin da uku ga watan Fabrairun bana.
Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a Muhammad Lawal Garba a jiya Talata ta ware gobe Alhamis a matsayin ranar da zata zauna kan bukatar da jam’iyyar ta PDPn ta shigar gaban ta.
A sakamakon zaben shugaban kasa da aka sanar hukumar INEC ta ayyana cewa shugaban kasa muhammadu Buhari ne ya lashe zaben bayan da ya samu kuri’u sama da miliyan goma sha biyar da dubu dari da casa’in da daya, inda abokin karawar sa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri’u sama da miliyan goma sha da dubu dari biyu da sittin da biyu.
Sai dai jam’iyyar ta PDP taki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar, inda tayi ikiraricn cewa dan takarar ta Atiku Abubakar ne ya samu nasara a zaben.