Manyan Labarai
Kotun Sojin Kamaru ta yanke wa jagoran ‘yan awaren kasar hukuncin daurin rai da rai
Kotun Soji a kasar Kamaru ta yanke wa jagoran ‘yan awaren kasar da wasu mukarrabansa hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da laifin ta’addanci da kuma raba kan al’ummar kasar.
Lauyan gwamnatin, Martin Luther ya shaida wa manema labarai cewa, an yanke wa Julius Sisiku Ayuk Tabe da wasu mabiyansa su 9 hukuncin daurin rai da rai, inda shi kuma lauyan ‘yan awaren, Joseph Fru ya caccaki hukuncin.
Kawo yanzu dai lauyan ‘yan awaren bai ce za su daukaka kara ba don kalubalantar hukuncin kotun sojin.
Ayuk Tabe danshekaru 54 da haihuwa kuma masanin fasahar kwamfuta, shi ne mutum na farko da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar Ambazonia wadda ta balle daga kasar ta Kamaru, sannan ta sanar da kafuwarta cikin watan Oktoban 2017 a yankunan masu magana da Turancin Ingilishi a kasar ta Kamaru.
Sai dai gwamnatin kasar ta Kamaru ta mayar da martani ta hanyar amfani da sojoji don murkushe yunkurin kafa sabuwar kasar ta Ambazonia.
Artabun da aka yi tsakanin bangarorin biyu, ya yi sanadiyar rasuwar mutane 1,850 kamar yadda kungiyar da ke sanya ido kan rikice-rikice ta kasa-da-Kasa, ICG ta bayyana, inda ita kuma majalisar dinkin duniya ta ce, mutane 530 sun bar muhallansu don gujewa tashin hankalin.