Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun tarayya ta umarci ƴan sanda da su bai wa wani mutum motarsa.

Published

on

Babbar Kotun tarayya da ke nan Kano ta umarci rundunar ƴan sanda da su bai wa wani mutum Ɗanjummai Ado Wudil motarsa.

Da ta ke yanke hukunci a yau mai shari’ar JE Inyang ta ce, kutsa kai da ƴan sandan suka yi gidan magidancin ba tare da izni ba ya saɓa da doka.

Sannan ta umarci a mayar masa da motarsa nan take tare da biyansa diyya.

Magidancin Ɗanjummai ya sayi motar ne bayan da ƴan sanda suka yi gwanjon kayayyakinsu, sannan suka bashi shaida.

Daga bisani kuma suka biyo shi har gida suka kwace motar bayan da ya fara amfani da ita.

Malam Ɗanjummai Ado Wudil ya bayyana Freedom Radio farin cikinsa.

Ya kuma yi godiya ga lauyansa Barista Abba Hikima Fagge.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!