Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Kowa ya je a yi masa allurar corona domin ba ta da wani illa – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci al’ummar kasar nan da su yi fitan dango don karbar allurar riga-kafin cutar covid-19.

A cewar sarkin na musulmi allurar rigakafin ce kawai mafita a halin da ake ciki wanda zai magance fargabar da ake yi game da cutar corona.

Sarkin na musulmi ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke jawabi a wajen wani taron wayar da kan malaman addinin musulunci da limamai wadda hukumar kula da lafiya a matakin farko ta shirya jiya a Abuja.

Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, ya kuma yi kira ga shugabannin addinai da na gargajiya da su rika wayar da kan magoya bayansu, kan muhimmancin yin rigakafin na cutar covid-19.

Kiran na sarkin musulmi na zuwa ne awanni kadan bayan fitar da sakamakon rahoton kwamitin bincike da hukumar kula da magunguna ta nahiyar turai ta kafa, kan zargin ko riga-kafin cutar ta corona samfarin Astrazeneca na da illa.

A cewar sakamakon rahoton kwamitin na tarayyar turai, fargabar da ake yi kan riga-kafin cutar ta covid-19, ta zo karshe, domin kuwa, binciken su ya gano cewa, babu illa a tattare da riga-kafin.

Wannan al’amari dai, ya sanya tuni kasashen turai da suka dakatar da amfani da riga-kafin na wucin gadi, suka janye matakin da suka dauka a baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!