Barka Da Hantsi
Kowa zai iya shiga tsarin inshorar lafiya, ba sai ma’aikacin gwamnati ba – Aminu Wudil
Shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta ƙasa reshen jihar kano ya ce kowa zai iya shiga tsarin inshorar lafiya ba sai ma’aikaci ba.
Alhaji Aminu Yusuf Wudil ne ya bayyana hakan, jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio da ya mayar da hankali kan muhimmancin inshorar lafiya ga ma’aikata.
“Tsarin inshorar kowa zai iya shiga walau me sayar da Yalo da masu ga ruwa, da ma duk wanda yake sha’awa ko kuma yake buƙatar samun sauƙi wajen harkokin lafiya”.
Wudil ya kuma ce “Muna ɗaukar nauyin duk wata lalura da ta tasowa duk wanda yayi rijistar inshora kuma komai yawan kuɗi muna ɗaukar nauyi amma ban da cutar HIV”.
Alhaji Aminu Yusuf Wudil ya yi kira da ga duk masu son shiga inshorar lafiya da ma waɗanda suke ciki kan cewa kofar su a buɗe ta ke na yiwa kowa rijista.
You must be logged in to post a comment Login