Labaran Kano
Koyar da Dalibai yadda za su Kula da Lafiyar su zai rage yaduwar cutuka- ARD
Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa wato Association of Resident Doctors reshen Asibitin Kashi na Dala ta ce, idan aka samar da wani tsari na musamman da za a rinka koyar da Dalibai tun daga makarantun Sakandare yadda za su Kula da kiwon Lafiyar su, hakan zai saka a rage yawan samun yaduwar cutuka a tsakanin al’umma.
Hakan na zuwa ne a wani Taron gangamin wayar da kan al’umma yadda za su Kula da Lafiyar su da kungiyar ta gabatar a makarantar Yan Mata ta GGSS Kofar Mazugal a cikin karamar hukumar ta Dala.
Haka zalika kungiyar ta ce, ‘yan Mata masu tasowa za su iya bin hanyoyi da dama domin Kula Da Lafiyar su musamman wajen tsaftace jikin su da dukkan a bubuwan da za su sanya lokacin da suke jinin Al’ada.
Da yake jawabi shugaban kungiyar a nan Kano Dakta Aliyu Nura Muhammad ya ce duk karshen shekara suna gabatar da bita kan kiwon Lafiya hakan ne yasa suka fara da makarantar.
Abdurrahman Junaidu shine mataimakin shugaban makarantar Yan matan ta GGSS Kofar Mazugal ya bayyana Jin dadin sa Kan yadda aka zabi makarantar tasu, ya Kuma ce za su ci gaba da wayar musu da Kai Kan muhimmancin Kula da Lafiya.
Wasu daga cikin daliban makarantar Yan matan ta GGSS Kofar Mazugal sun bayyana Jin dadin su, da Cewa za suyi amfani da Bitar da Likitocin sukai musu.
Kungiyar Likitocin masu neman kwarewar dai ta ce a mako Mai zuwa za ta gudanar da ayyuka ga Marasa Lafiya tare da basu magunguna kyauta.
You must be logged in to post a comment Login