Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kuɗin da aka tura a asusun ƴan fansho a watan nan ba zai isa a biya su ba  – ƙungiyar ƴan fansho

Published

on

Ƙungiyar ƴan fansho ta ƙasa reshen jihar Kano ta ce, kuɗin da ya shigo asusun yan Fansho daga ƙananan hukumomi na wannan watan, ba zai taba isa a biya ƴan fansho gaba ɗaya ba.

Shugaban ƙungiyar kwamared Salisu Ahmad Gwale ne ya bayyana hakan, jim kaɗan Bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom Radio.

Kwamared Salisu Ahmad ya ce “ba daidai ba ne ma’aikaci ya gama aikin sa, ba tare da an biyashi hakkokin sa ba, kuma wannan matsala tra faru samuwa ne tun daga lokacin da aka samar da dokar ƴan fansho a shekarar 2007.

“Mu shugabannin ƙungiyar ƴan Fansho muna nesanta kan mu da yadda ake samun matsalaa ɓangaren biyan ƴan Fansho haƙƙokin su a yanzu” inji Kwamare Gwale.

Kwamared Salisu Ahmad Gwale ya ce, za a iya gyara matsalar ta hanyar kowacce ma’aikata ta riƙa bayar da kuɗaɗenta don biyan ƴan fanshon.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!