Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kuɗin makamai: Majalisa ta nemi babban hafsan soji ya gurfana a gaban ta

Published

on

Majalisar wakilai ta ce wajibi ne babban hafsan sojin kasa na kasar nan laftanal janar Attahiru Ibrahim ya gurfana gaban kwamitinta don ya yi karin haske game da zargin badakala a cinikin makamai.

A Jiya juma’a ne dai kwamitin wucin gadi na majalisar ta wakilai da ke bincikar cinikin makamai ya ki amincewa da wakilcin da babban hafsan sojin ya tura a zaman da kwamitin ya yi.

Tun farko dai dan majalisa Bede Eke daga jihar Imo shine ya gabatar da bukatar tursasa babban hafsan sojin kasar da ya gurafana gaban kwamitin shi da kansa sabanin tura wani na kasa da shi ya wakilce shi.

Yayin zaman kwamitin na jiya dai, ‘yan majalisar sun ki tattauna lamarin da manjo janar Charles Ofoche wanda ya wakilci babban hafsan sojan kasar.

Wannan na zuwa ne a lokaci guda da zargin badakalar cinikin makamai ya sake bulla sakamakon zargin da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Manjo janar Badagana Monguno ya yi ga tsofaffin manyan hafsoshin tsaro, ko da ya ke daga bisani ya musanta kalaman, yana mai cewa ba a fahimci abin da yak e nufi ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!