Labaran Kano
Ku kasance masu yin kasuwanci kamar yadda addinin musulunci ya koyar
An shawarci ‘yan kasuwa da sauran ma’aikata da su kasance masu gudanar da harkokin kasuwancinsu irin yadda addinin musulunci ya koyar domin kaucewa fadawa cikin fushin ubangiji a ranar gobe kiyama.
Shugaban cibiyar koyar da zaman Aure da kasuwanci a addinin Musulunci Dakta Yahya Tanko ne ya bayyana hakan yau lokacin taron bita tare da wayar da kan ‘yan kasuwa da ma’aikata kan tarbiyyar addinin musulunci a cikin harkokin kasuwanci.
Ya kara da cewa abin takaici ne yadda ‘yan kasuwa a yanzu suke gudanar da harkokin kasuwancin su, wanda hakan ya sauka daga layin koyarwa irin ta addinin musulunci.
A cewar Dakta Yahya Tanko kamata ya yi duk wani musulmi a ko ina yake ya zama tamkar mudubi da kowacce al’umma zata rika koyi da shi ta fuskar kasuwanci.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa malamai da ‘yan kasuwa da ma’aikata da dama ne suke halarci taron.