Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ku riƙa taimakawa talakawa – Saƙon Sarkin Kano ga ƴan Kwallon Ƙafa

Published

on

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira da ƴan ƙwallon kafa da su yi ko yi da kyauwawan halayen shugaban ƴan wasan super eagles Ahmed Musa na taimakawa al’umma musamman marasa ƙarfi.

Sarkin ya yi wannan kira lokacin da shugaban ƴan wasan kwallon ƙafa na super eagles da takwaransa Shehu Abdullahi bisa jagorancin Ibrahim Buba Galadima suka ziyarce shi a radar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana farin cikinsa bisa ziyarar tare da shawartar ɗan wasan kwallon kafa Ahmed Musa daya rikya amfani da irin kayan sawar Hausawa don nuna al’ada ga ƴan baya.

A nasa jawabin shugaban ƴan wasan kwallon ƙafa ta ƙasa super eagles Ahmed Musa ya ce, yaje fadar ne don neman tabarrakin sarki da addu’a kan abubuwan alherin daya sanya a gaba.

Ahmed Musa ya kuma ce, nan bada daɗewaba zai taimakawa ƙananan hukumomi arba’in da huɗu da ke jihar Kano musamman a ɓangaren lafiya ta hanyar Kai musu magunguna don taimakawa al’umma.

Wakilin mu na masarautar kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karɓi baƙonci mai martaba sarkin Ringim da ke jihar Jigawa Alhaji Sayyadi Muhmud.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!