Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Ku rika-taka-tsan-tsan,  don ba za mu iya bai wa duk makarantu tsaro ba, gwamnati, ga iyayen yara

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce akwai bukatar al’ummar kasar nan baki daya da su rika kula sosai wajen sanya idanu don kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga da ke sace dalibai a kasar nan.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya bayyana haka yayin zantawa da jaridar Punch, a jiya litinin, yana mai cewa gwmanatin tarayya ba za ta iya samar da tsaro a dukkan nin makarantun kasar nan ita kadai ba.

A cewar sa, gwamnati ta bai wa makarantun kasar nan umarni da su rika aikawa da rahoton duk wani lamari da basu fahimce shi ba, wadanda suka ga sana alaka da harkokin rashin tsaro.

Mista Nwajiuba ya kuma ce kusan kafatanin makarantun kasar nan suna da Katanga da ta kewayesu, in ban da kadan daga cikin wasu makarantun jihohi.

Wannan na zuwa ne a lokaci guda da ‘yan bindiga ke ci gaba da sace dalibai a arewacin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!