Connect with us

Addini

Ku rika tallafawa marasa galihu – Dagacin Sharada ga masu hannu da shuni

Published

on

Dagacin Sharada Alhaji Ilyasau Mu’azu Sharada ya bukaci al’ummar musulmi da su sadaukar da wani bangare na dukiyarsu domin tallafawa mabukata.

Alhaji Ilyasu Mu’azu Sharada ya bayyana hakan ne a yayin taron rabon kayan abinci ga marayu dari hudu da gidauniyar Kano Network mai tallafawa marayu dake Unguwar Salanta ta gudanar a makarantar Firamare ta Salanta.

Sannan kuma ya yi kira ga kamfanonin dake Sharada da ba sa taimakawa jama’a da su dage wajen bayar da na su taimakon.

Da yake jawabi shugaban gidauniyar Malam Adam Umar Abu Salim, ya bayyana cewa sun yi rabon kayan tallafin ne don tallafawa marasa galihu.

Wakilinmu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa an raba kayan abinci da suka hadar da shinkafa da taliya masara da gero da sukari da kuma magunguna, inda a gefe guda kuma wata mata ta bayar da gudunmawar kudi naira miliyan daya domin rabawa mata jari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!