Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ku zakulo ‘yan IPOB da suka kai hari kan ‘yan sanda, gidan yari a Owerri – Muhd Adamu

Published

on

Sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan Mohammed Adamu, ya tabbatar da cewar ‘yan kungiyar tsagerun dake rajin kafa ‘yan-tacciyar kasar Biafra, ta IPOB ta hannun haramtacciyar kungiyar tsaronsu ta Eastern Security Network, su ka kai hari a garin Owerri na jihar Imo a daren jiya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar nan Frank Mba, ya sakawa hannu, ta ruwaito sufeto janar na ‘yan sandan na kuma umartar da tura karin dakarun kwantar da tarzoma, don tabbatar da wanzar da zaman lafiya da samar da tsaro.

A cewar sanarwar Muhammad Adamu, ya umarci Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, da ya zakulo tsagerun IPOB, da suke da hannu wajen kai harin.

Rahotanni sun ce maharan, sun kone motoci da dama, tare da sakin daurarru dake gidan gyaran hali na Owerri su 1,500, a harin da suka kai na safiyar yau Litinin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!