Labarai
Kudin makamai: Majalisar dattijai ta gayyaci babban hafsan sojin kasa da ministar kudi
Ma’aikatar kudi ta tarayya ta shaidawa kwamitin kula da rundunar sojin kasar nan na majalisar dattijai cewa gwamnatin ta kashe naira biliyan dari da casa’in da takwas da miliyan tamanin da hudu wajen yaki da ta’addanci daga shekarar 2019 zuwa yanzu.
Babban sakatare mai kula da ayyuka na musamman a ma’aikatar kudi Alhaji Aliyu Shinkafi ne ya bayyana haka, yana mai cewa, duk kudaden da aka amince a kashesu don yaki da ta’addanci an mikasu ga rundunar sojin kasar nan.
A cewar sa, ma’aikatar ta bai wa sojojin naira biliyan saba’in da biyar a shekarar dubu biyu da goma sha tara.
Sai dai ya yin da ya ke wannan jawabi ne sai shugaban kwamitin kula da rundunar sojin na majalisar dattijai, Sanata Ali Ndume ya fitar da wata takarda wanda ya ce ta fito ne daga ofishin babban hafsan tsaron kasar nan wanda ke korafin cewa, rashin sakin naira biliyan hamsin da ma’aikatar kudi ba ta yi ba, shi ya haifar da tsaiko a yaki da su ke yi da ta’adanci
Saboda haka ne kwamitin ya bukaci ministar kudi Zainab Ahmed da babban hafsan sojin kasa na kasar nan laftanal janar Attahir Ibrahim da su gurfana gaban kwamitin don fayyace inda aka yi aka haihu a ragaya kan wannan batu.
You must be logged in to post a comment Login