Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Turmutsitsi: Mutane 44 sun mutu a wajen bautar Yahudawa a kasar Isra’ila

Published

on

Akalla mutane 44 ne suka rasa rayukansu ya yin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani turmutsitsi da ya faru a wajen bautar mabiya addinin yahudawa a kasar Isra’ila.

Rahotanni sun ce turmutsitsin ya faru ne da safiyar yau juma’a, a wani yanki da ke arewacin kasar wanda kuma tuni wasu mutane 150 suka samu munanan raunuka.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar Isra’ila David Adom, ya ce tuni aka garzaya da gawarwakin da kuma wadanda suka jikkatar zuwa asibiti

A tabakin mai magana da yawunsa Zaki Heller, cikin mutane 150 da suka jikkatar guda 6 suna halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Firaministan kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana lamarin a matsayin wani balahira da ya shafi kasar, inda ya yi addu’ar samun lafiya ga wadanda suka jikkata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!