Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Kula da tsaftar muhalli zai hana yaduwar cutar Corona-KIWMA

Published

on

Cibiyar rajistar ma’aikatan muhalli ta kasa ta yi kira ga al’ummar kasar nan da su rinka tallafawa gwamnati da kungiyoyin al’umma wajen kula da tsaftar muhalli yadda ya kamata, don magance cututtuka a cikin al’umma, musamman ma a wannan lokaci da cutar Corona ta addabi duniya.

Babban jami’in cibiyar mai kula da shiyyar Arewa maso yamma Bala Muhammad Tukur ne ya bayyana hakan, yayin gudanar da wani aikin feshin maganin kashe cututtuka a gidajen Gyaran hali na Goron Dutse da Kurmawa, da hadin gwiwar kungiyar kamfanoni masu zaman kansu da kula da tsaftar muhalli na Kano.

Ya kara da cewa kungiyoyin sun sha alwashin ci gaba da gudanar da feshin maganin a cikin kasuwanni da masana’antu da wuraren tsare masu laifi, don magance yaduwar cutuka musamman a wannan lokacin da ake fama da cutar Corona.

A na sa jawabin mataimakin Kwamturona mai kula da gidan gyaran hali a nan Kano Alhaji Ibrahim Idris, bayyana jin dadinsa ya yi bisa aikin feshin da cibiyar ta gudanar tare da kira ga kungiyoyin al’umma da su rinka tallafawa gwamnati wajen magance cutuka a kasar nan.

Cibiyar ma’aikatan muhallin ta kasa da kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta Kano sun gudanar da feshin maganin a dakunan kwanan wadanda aka tsare din da bandakuna da filayen wasanni da motocin daukar daurarrun da kuma harabar gidajen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!