Connect with us

Labaran Kano

Rundunar ‘yan sanda ta yi wawan kamu a Kano

Published

on

Jami’an rundunar yansandan Jihar Kano ta kama direban Adai-daita Sahu da ake  zargin yana jigilar masu kwacen wayoyin salula na hannu ta hanyar amfani da mugan makami.

Kakain rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a yayin zantawa da wakilin mu Abba Isa Muhammadu cewa  yana daukar masu kwacen ne ya kuma kaisu guraren da suke tare mutane su zare musu wuka ko almakashi daga bisani kuma sai a su kwace wayar.

DSP Abdullahi Haruna ya kuma kara da cewar cikin wadanda yake dauka aikata mumunan aikin sun hada da Abba Bros da Jiniyo, da kuma Turmi.

Yana mai cewar dukkanin su na zaune a unguwannin Sharada da Tukuntawa a karamar hukumar Birni da kewaye.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!