Labarai
Kungiyar Amnesty international ta ce sojojin kasar nan sunyi biris da gargadin boko haram
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce Sojojin Kasar nan sun yi biris da gargadin cewa ‘yan Boko Haram za su kai hari, sa’o’i kalilan gabanin sace ‘yan matan sakandaren Dapchi sama da 100.
Yau wata guda kenan da mayakan Boko Haram suka sace ‘yan matan a lokacin da suke makaranta a garin Dapchi na Jihar Yobe.
Amnesty ta kara da cewa yawancin shugabannin al’ummar yankin, sun sanar da Sojoji tun lokacin da suka samu labarin jerin gwanon Motocin maharan na wani kauye mai nisan kilomita 30 daga garin na Dapchi, kwana guda gabanin sace ‘yan matan.
Sun yi ikirarin ko a lokacin da maharan suka isa garin an sanar da Sojojin, amma ba su dauki wani mataki a kai ba.
Rundunar Sojin kasar nan ta ce tuni gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai yi kwakkwaran bincike kan gazawar jami’an tsaro a yankin da ta kai ga sace matan.
Kawo yanzu iyayen ‘yan Makarantar na zaman zullumi da tashin hankalin rashin sanin ainahin inda ‘ya’yansu suke.
Sama da shekara Hudu kenan da sace ‘yan matan Sakandaren Chibok sama da 200 da Boko Haram ta yi, gwamnatin tarayya ta kubutar da wasu daga ciki ta hanyar amfani da tattaunawa tsakanin ta mayakan bisa jagorancin kungiyar agaji ta Red Cross, kuma kawo yanzu sama da 100 ba a kubutar da su ba.