Connect with us

Labarai

Rundunar sojan saman kasar nan ta dakile harin Boko Haram

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta samu nasarar dakile wani yunkurin hari da mayakan Boko Haram su ka yi kokarin kai wa a garin Michika da ke jihar Adamawa.

Rahotanni sun ce, ‘yan Boko Haram din sun iso garin ne ta cikin motoci kirar Toyota Hilux da kuma Babura masu yawa da misalin karfe shida na maraicin jiya, inda daganan ne suka rika dauki ba dadi da siojoji har na tsawon awanni biyu kafin daga bisani su tsere.

Wata mazauniyar garin na Michika mai suna Maryam Malama, ta ce, da farko ‘Yan Boko Haram din sun yi kokarin cin karfin sojojin da ke zaune a wajen wani shingen bincike da ke daf da garin, sai dai jajircewa da sojojin su ka yi, ya sanya su ka koma da baya kafin daga bisani wasu sojojin su ka kawo musu dauki.

Akwai yiwar sake kai hari a Sakandiren ‘yan mata na Dapchi

Buhari yafi kowa sanin matsalar tattalin arzikin Najeriya -Sunusi Tambari Jaku

Kungiyar boko haram ta kai hari karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa

Haka zalika wani dan kungiyar sintiri na Vigilante a yankin ya shaidawa manema labarai cewa, ya ga gawarwakin ‘yan Boko haram da dama a yashe wadanda sojojin suka kashe.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,751 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!