Kiwon Lafiya
Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bukaci su rinka sigowa ana damawa dasu
Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bayyana bukatar dake akwai wajen mutane su rinka shigowa ana damawa dasu a yayin gudanar da ayyukan su.
Babban jami’in shiyya na kungiyar ta Red Cross anan Kano, Alhaji Musa Abdullahi ne ya bayyana haka, yayin tattaunawa da wakilin Freedom rediyo Umar Idris Shuaibu a wani bangare na bikin ranar kungiyar agaji ta Red Cross ta duniya.
Ya ce suna bukatar gwamnati da ta tallafa musu wajen koyar da matasa dabarun bada taimakon farko a yayin wani hatsari.
Alhaji Musa Abdullahi ya kuma ce, abune mai kyau jama’a su samu ilmin da za su rika bada agajin gaggawa a lokacin da wani hatsari ya faru.
Bikin ranar dai ana gudanar da shi ne kowacce 8 ga watan Mayu, don tunawa da lokacin da Henri Dunant ya kirkiri kungiyar ta Red Cross a shalkwatar ta dake Geneva a kasar Switzerland.