Kiwon Lafiya
Kungiyar bibiyar yada za’a mika mulki ta fitar da rahoto na farko na zabe
Kungiyar bibiyar yadda za’a mika mulki ta Transition Monitoring Group ta fitar da rahoton farko na yadda aka gudanar da babban zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki ta kasa wanda aka yi a ranar Asabar 23 ga wannan watan.
Sanawar wace aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun hadin gwiwar kungiyoyin Transition Monitoring da kuma ta Human and Environmental Development Agenda cewa rahoton farkon masu sanya idano kan zaben suka bayar shi ne wanda aka tantance irin yadda aka gudanar da zaben.
A cewar kungiyar yadda al’umma suka fito don kada kuri’un su abun a yaba ne, da yadda aka dauki matakan tsaro da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar da zaben.
Masu sanya idano da dama ne dai aka rarraba jihohin 36 dake fadin kaar nan da kuma babban birnin tarayya Abuja.