Connect with us

Kiwon Lafiya

Baturen zabe sanata ta gabashin jihar Ogun ya ce ba’a kammala zaben sanata ba

Published

on

Baturen zabe na mazabar sanata ta gabashin jihar Ogun Farfesa Chris Nwoka ya bayyana cewa ba’a kamamla zaben sanata a yankin ba.

A yayin da ake tattara sakamakon zaben na kananan hukumomin 9 na yankin jam’iyyar APC ta sami kuri’un dubu tamanin da hudu da dari tara da Ashirin da tara yayin da jam’iyyar PDP kuwa ta sami kuri’u Dubu Tamanin da biyu da dari hudu da Hamsin da bakwai.

Farfesa Chris Nwoka ana gab da za’a sanar da cewa dan takarar jam’iyyar APC sanata Mustapha Olaleken ne ya lashe zaben sai magoya bayan abokin takarar sa  na jam’iyyar PDP Sosanwo Ayoola suka tada hargitsi.

Haka zalika kuma an soke zabe a mazabo 10 dake yankin karamar hukumar Ijebu ta gabas dake jihar Ogun, bayan da aka sami banmbaci mai yawa na yawan masu kada kuri’u da kuma yawan al’ummar dake yankin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,813 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!