Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar bibiyar yada za’a mika mulki ta fitar da rahoto na farko na zabe

Published

on

Kungiyar bibiyar yadda za’a mika mulki ta Transition Monitoring Group ta fitar da rahoton farko na yadda aka gudanar da babban zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki ta kasa wanda aka yi a ranar  Asabar 23 ga wannan watan.

Sanawar wace aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun hadin gwiwar kungiyoyin Transition Monitoring da kuma ta Human and Environmental Development Agenda cewa rahoton farkon masu sanya idano kan zaben suka bayar shi ne wanda aka  tantance irin yadda aka gudanar da zaben.

A cewar kungiyar yadda al’umma suka fito don kada kuri’un su abun a yaba ne, da yadda aka dauki matakan tsaro da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar da zaben.

Masu sanya idano da dama ne dai aka rarraba jihohin 36 dake fadin kaar nan da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!