Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ni zan jagoranci yaki da Boko Haram- Janar Tukur Burutai

Published

on

Babban hafsan soji na kasa Janar Tukur Yusuf  Buratai, zai koma yankin   Arewa maso gabashin kasar nan, don cigaba da jagoranta da gudanar da aikin Sojin kasar nan da kuma yaki da ‘yan Boko Haram.

Janar Burutai, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga Sojin kasar nan na musamman na Special Super Camp, dake garin Ngamdu a karamar hukumar  Kaga dake jihar Borno, inda ya shaida musu cewar’ daga yanzu zan kasance tare daku a dukkan kowanne filin daga’.

A wata takarda, da kakakin sojin kasar nan Kanal Sagir Musa, ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai, ta sanar da cewa a baya  babban hafsan Sojin , ya shiga cikin tawagar da ta kai ziyara ga tawagar sojin  da take a gurare daban –daban da suke a gabashin kasar nan wanda ke aikin samar da tsaro a yankin.

Labarai masu alaka.

Rundunar sojan saman kasar nan ta dakile harin Boko Haram

Sojojin Najeriya na fafatawa da yan kungiyar boko haram a jihar Borno

Sanarwar ta kara dacewa, Burutai, ya kai ziyara a sansanin Soji na daya,  dake  Mulai, da sansani na sha biyu na  sojoji na musamman dake Chabbol kusa da birnin  Maiduguri, in da ya tattauna dasu tare da yi musu jawabi.

Sanarwar, ta tabbatarwa da al’ummar kasar nan cewa rundunar sojin kasar nan a shirye take data kare rayuka da dukiyoyin jama’a da iyakokin kasar nan a koda yaushe, tare da alwashin kawo karshen ta’addancin ‘yan kungiyar ISWAP,dana Boko Haram, nan ba da dadewa wa ba yankin Arewa maso gabashin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!