Labarai
kungiyar Boko Haram ta tuntube ni kan ‘yan matan sakandaren Dapchi- Aisha Wakil
‘yar fafutukar kare hakkin dan adam Aisha Wakil ta yi ikirarin cewar wani bangare na kungiyar Boko Haram ya tuntube ta inda suka sanar da ita cewar yan matan sakandaren Daochi dake jihar Yobe su dari da goma na hannun su.
Aisha Wakil wadda aka fi sani da Mama Boko Haram, na daya daga cikin mambobin kwamitin tattaunawa da samar da zaman lafiya tare da harkokin tsaro a arewacin kasar nan wanda aka kafa zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Yayin wata ganawa da kamfanin dallancin labarai na kasa Aisha Wakil ta ce kungiyar bangaren Barnawi su ne suka yi mata waya.
Ta kuma ce sun fada mata cewar babu abin da ya sami yan matan kuma cikin koshin lafiya da kyakkyawan yanayi.
A wata zantawa da kafar labarai ta PR Nigeria cikin wannan mako, Aisha Wakil ta yi kira ga yayan kungiyar su taikama su saki yaran domin su koma wurin iyayen su.
Yar gwagwarmayar wadda ke da hanyar zantawa da kungiyar ta Boko Haram da wasu shugabannin ta, ta ce a shirye take ta sadaukar da ranta domin kubutar da yan matan na Dapchi.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta fitar yau juma’a, ta ce ta fadada aikin binciken inda yaran suke har zuwa kasashen dake makwabtaka da Najeriya.