Labaran Wasanni
Kungiyar Chan Eagles ta samu nasarar zuwa zagayen quarter final a wasa kasashen nahiyar Afrika
Kungiyar kwallon kafa ta kasa ta ‘yan wasa ma su taka leda a kungiyoyin cikin gida CHAN Eagles, ta sami nasarar zuwa zagayen kusa da kusa dana karshe watau quarter final bayan da kungiyar ta doke takwararta ta kasar Equatorial Guinea da ci uku da daya.
Wakilin mu na fagen wasanni Abubakar Musa Labaran ya ruwaito cewa kungiyar ta CHAN Eagles ce ke kan gaba a rukuni na C.
A wasan da Najeriya ta yi na farko a gasar da kasar Rwanda sun tashi kowa na nema sannan da ta doke libiya da ci daya da nema ya yin da a jiya Najeriya ta ragargaji Equatorial Guinea da 3 -1
A gasar Firimiya ta kasa kuwa wasannin da zasu gudana a yau.
Wasan sada zumunci da suke gudana a birnin Kano da kewaye kuma.
A wani labarin hukumar kwallon kafa ta kasar Burtaniya ta sanar da Phil Neville a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila ta mata wanda zai jagoranci kungiyar zuwa shekarar 2021.
Phil Neville, mai shekara 41, ya horas da kungiya Manchester United da Valencia da kuma kungiyar ‘yan wasan kasar Ingila ‘yan kasa da shekaru 21.
Daga bangaren tennis kuma ‘yar wasa ta daya a duniya Simona Halep ta samu nasarar zuwa zagayen na kusa dana karshe a gasar Australian Open bayan da ta doke Karolina Pliskova.
Halep yar kasar Italiya mai shekaru 26,ta yi nasar a wasannin 9 da ta kara inda ta yi nasara da ci 6-3 6-2.
Yanzu Halep zata kara da Angelique Kerber bayan da Kerber ta doke Madison da ci 6-1 6-2.
Haka zalika Chung Hyeon ya yi nasara zama dan wasan kasar Korea ta kudu na farko da halarci wasan kusa da na karshe watau Grand Slam semi-final bayan da ya doke dan kasar Amurka Tennys Sandgren a gasar Australian Open da ci 6-4 7-6 6-3.