Connect with us

Kiwon Lafiya

Kungiyar ECOWAS ta koka kan yaduwar kananan makamai sama da miliyan 10 a yammacin afurka

Published

on

Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin afurka wato (ECOWAS), ta ce, kananan makamai sama da miliyan goma ne ke hannun jama’a ba bisa ka’ida ba a yankin na yammacin afurka.

Shugaban sakatariyar kungiyar Mr. Jean Claude Brou ne ya bayyana haka ga manema labarai yayin wani taro kan yankin Sahel.

Jean Claude Brou wanda kwamishina mai kula da harkokin siyasa, tsaro da zaman lafiya Francis Behanzin ya wakilta, ya ce, wajibi ne hukumomin da lamarin ya shafa su dauki mataki don dakile ci gaba da yaduwar su.

Ya kuma alakanta yawaitar makamai a hannun jama’a ba bisa ka’ida ba, da cewa, shine sanadiyyar rikice-rikice da kashe-kashen ta’addanci da ake samu a yankin.

Shugaban sakatariyar kungiyar ta ECOWAS ya kara da cewa, rashin ci gaban kasashen yankin musamman rashin aikin yi da ya yi katutu tsakanin matasa da kuma karin adadin jama’a da ke karuwa, yana kara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin na yammacin afurka.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!