Kiwon Lafiya
Kungiyar Hand in Hand ta bukaci kungiyoyin goyon bayan shugaba Buhari su ci gaba da yada ayyukan sa
Kungiyar Hand in Hand Buhari Orgnization ta bukaci daukacin kungiyoyin da ke goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari su himmatu wajen yada irin ayyukan Alherin da Shugaban kasar ke gudanarwa a Najeriya domin ciyar da kasar gaba.
Jami’in shiyya na kungiyar Ahaji Ibrahim Usman ne ya yi wannan kira a yau Alhamis ya yin taron masu ruwa da tsaki na kungiyar ta da ya gudana a nan jihar Kano.
Alhaji Ibrahim Usman, ya kuma bukaci daukacin yan Nigeria da su kadawa shugaba Buhari kuri’ar su domin ci gaba da yada irin ayyukan da shugaban Kasar ya ke gudanarwa a halin yanzu.
A cewar sa akwai ayyuka da gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ta samarwa ‘yan Nigeria, da suka hadar da samar wa matasa ayyunkan yi, da inganta kiwon lafiya, da kuma samar da ingantaccen ruwan sha da sauran abubuwa more rayuwa.
Alhaji Ibrahim Usman, ya kuma musanta kalaman da wasu ke yi na cewa, sun zabi dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a matsayin zabin ‘yan Arewa cin Najeriya da cewar ba gaskiya bane, a cewar sa shugaba Muhammadu Buhari shi ne dan takarar daya tilo da al’ummar Arewacin Najeriya nan suka yadda da shi.
Ya kuma ce mutanen da ke ikirarin kansu dattawan Arewa babu abinda suka yiwa yankin Arewacin Najeriya da ke nuna ciyar da yankin gaba, musamman ma lokacin da suke kan madafun iko.