Kiwon Lafiya
Kungiyar IPMAN:akwai bukatar rushe wasu gidajen mai a kasa baki daya
Kungiyar Dillalan mai ta kasa IPMAN ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rushe gidajen mai sama da dubu biyu da aka ginasu ba akan ka’ida ba domin magance matsalar karancin mai a fadin kasar nan.
Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Alhaji Aminu Abdulkadir ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai a fadar shugaban kasa ta Asorok jiya a Abuja.
A cewar sa idan har gwamnati da gaske take tana son magance matsalar karancin mai to kuwa ya zama wajibi ta dauki matakin rushe gidajen man wadanda ya yi zargin cewa suna taka rawa wajen ta’azzara matsalar karanci mai a kasar nan.
Alhaji Aminu Abdulkadir wanda yayi jawabin jim kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari ya jagoranta, ya ce; ba ko shakka gidajen man na bogi sune silar karkatar da man fetur da ake rabawa.
Ya ce akwai damuwa matuka ganin yadda wasu Dillalan mai wadanda basu da lasisi amma sai gansu da mai yayin da a bangare guda Dillalan mai da ke da lasisi basa samun man.