Kiwon Lafiya
Kungiyar JOHESU ta gargadi al’umma da su daina zuwa asibitocin gwamnati
Hadakar kungiyar ma’aikatan lafiya ta kasa JOHESU ta gargadi al’ummar kasar nan da ke ci gaba da zuwa asibitocin gwamnati domin duba lafiyar su da su daina yin hakan.
Kungiyar ta ce asibitocin sun zama kwangwaye sakamakon yajin aikin da suke yi.
Da yake karanta sanarwar da kungiyar ta fitar ga manema labarai, daya daga cikin jagororin kungiyar Dr. Godswill Okara, ya ce; ma’aikatan lafiya da shugabannin asibitocin kasar nan su ka yi hayar su domin cike gibin da mambobinsu su ka bari a dalilin yajin aikin ba kwararru bane.
Dr. Godswill Okara ta cikin sanarwar dai, ya kuma zargi ma’aikatar lafiya da rura wutar rikicin da ke ci gaba da faruwa tsakanin su.
Kungiyar JOHESU ta cikin sanarwar dai, ta ce ba gudu ba ja da baya kan matakin da ta dauka na shiga yajin aikin kuma ba ta tsorata ba kan matakin da gwamnati ta dauka na ba aiki ba albashi.