Labarai
Kungiyar KASSOSA ta gudanar da taronta na shekara a jihar Jigawa
Kungiyar tsoffin daliban kwalejojin kimiyya ta jihar Kano KASSOSA ta gudanar da babban taronta na shekara a jihar Jigawa, sabanin jihar Kano, Kamar yadda aka saba gudanarwa.
Da yake jawabi a wajen taron Mukaddashin Gwamnan Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ya jaddada aniyar gwamnatin jihar Kano na ci gaba da tallafawa sha’anin karatun kimiyya a jihar Kano don samar da ci gaba mai dorewa a fannonin daban-daban.
Alhaji Nasir Yusuf Gawuna Ya ce akwai bukatar ‘yan kungiyar su hada guyiwa wajen samar da daftarin da zai kawo ci gaban Kano a bangarori daban-daban, musamman ma bangaren ilimin kimiyya.
A nasa bangaren shugaban kungiyar tsoffin daliban kwalejojin kimiyya na kasa KASSOSA Alhaji Mustapha Nuhu Wali ya ja hankalin ‘ya’yan kungiyar wajen taimakawa junan su, da kuma kungiyar don ci gaba da tsayawa da kafar ta.
KASSOSA za ta gudanar da taron ta shekara a jihar Jigawa
Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito sakataren kungiyar KASSOSA Alhaji Hassan Abdulhamid Hassan ya yi kira ga kungiyoyin ajujuwa da su yi dukkan mai yiwuwa wajen hada guyiwa da uwar kungiyar don samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa a kwalejojin kimiyya dake jihar Kano.