Labarai
Kungiyar kwadago ta ayyana tafiya yajin aiki a fadin Nijeriya
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero ya umarci ma’aikatan gwamnati a kasa da su fara yajin aiki daga ranar Larabar makon gobe.
Ya kuma ba da umarnin cewa gamayyar kungiyoyin da suka kafa kungiyar kwadago ta Nijeriya su kuma za su kasance cikin shiri domin yin zanga-zanga a dukkan sassan babban bankin Nijeriya CBN.
Umarnin ya biyo bayan wa’adin farko da mambobin kwamitin na NLC suka fitar a makon jiya inda suka soki manufofin gwamnatin tarayya na sauyin kudi.
Ya kara da cewa duk da hukuncin da kotun koli ta bayar na barin tsofaffin naira 500 da naira 1000 su rika yawo da sabbin takardun har zuwa ranar 31 ga watan Disamban shekarar da muke ciki, lamarin ya kara ta’azzara saboda ma’aikata ba sa iya samun kudi don biyan bukatun su.
You must be logged in to post a comment Login