Labarai
Kungiyar Kwadago sun cimma yarjejeniya da Gwamnati
Gwamnatin tarayya ta ce ta cimma yarjejeniya da gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar nan game da yadda za a aiwatar tsarin biyan mafi karanci albashi ga ma’aikatan kasar nan.
Rahotanni sun ce an cimma yarjejeniyar ce, bayan kwashe tsawon awanni ana tattaunawa a daren jiya zuwa wayewar garin yau, Juma’a.
Ministan kwadago da samar da aikin yi, Dr. Chris Ngige ne ya bayyana haka ga manema labarai da safiyar yau juma’a.
A cewar ministan, gwamnati da gamayyar kungiyoyin kwadago, sun amince da tsarin da za a yi amfani da shi wajen karin albashi ga sauran ma’aikata da basa matakin naira dubu talatin.
Ita dai kungiyar kwadago tun farko ta bukaci yin karin kaso ashirin da tara ga albashin ma’aikata da ke mataki na bakwai zuwa goma sha hudu, yayin da ta bukaci karin kaso ashiriin da hudu ga wadanda ke matakin albashi na goma sha biyar zuwa goma sha bakwai.
NLC:sunyi barazanar tsunduma yajin aikin gama gari
NLC da wasu kungiyoyi sun shawarci gwamnati kan kudaden Paris Club
Shugaba Buhari ya taya shugaban kungiyar kwadago murna lashe zabe
Sai dai da ya ke zantawa da manema labaran, Dr Chris Ngige, ya ce, sun cimma yarjejeniyar yin karin kaso ashirin da uku ga ma’aikata da ke matakin albashi na bakwai yayin da wadanda ke matakin albashi na takwas za su samu karin kaso ashirin.
Sauran sune masu matakin albashi na tara wadanda za su samu karin kaso goma sha tara, sai wadanda ke matakin albashi goma zuwa goma sha hudu an yi musu karin kaso goma sha shida sai kuma ma’aikatan da ke matakin albashi goma sha biyar zuwa goma sha bakwai wadanda aka yi musu karin kaso goma sha hudu.
Tun a watan Afrilun bana ne dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya hannun kan dokar fara biyan mafi karancin albashin.